Taron ECOWAS na duba batun zabe a Mali

Shugaban kungiyar ECOWAS Alassane Ouattara
Image caption Taron ECOWAS ko CEDEAO ya jaddada cewa shiyyar na fuskantar matsalar tsaro

Shugabannin kasashen Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, wato ECOWAS sun shiga yini na biyu a taron da suke yi a Abuja.

Shugabannin na duba hanyoyin da za su kara taimakawa wajen ganin an gudanar da zabe a kasashen Mali da Guinea Bissau.

Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Alassane Ouattara ya jinjina wa kasashen Afrika da na yammacin duniya, wadanda suka taimaka wajen kwato Mali daga hannun 'yan tawaye.

Hakan a cewarsa ya samar da nutsuwar da ake da ita yanzu a kasar.

Saboda haka wajibi ne su ba da kowace irin gudummuwa, domin kafa gwamnatin dimokradiyya a kasar.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka, wajen cike gibin dala miliyan 25 da ake bukata wajen samar da kayan aiki da sauran dawainiyar zabe a Mali.

Wasu masu sharhi kan al'amurran nahiyar Afrika na ganin an yi gaggawa game da zaben na Mali.