Indiya ta sa doka kan sayar da ruwan batir

Wata Indiya da aka watsa wa ruwan batir
Image caption Wata Indiya da aka watsa wa ruwan batir

Kotun kolin Indiya ta umarci gwamnatin tarayyar kasar da na jihohi su sanya dokar sa ido a kan yadda ake sayar da ruwan batir, a wani yunkuri na rage harin da ake kaiwa mata.

Kotun ta ce za a sayar da ruwan batir din ne kawai ga mutanen da ke da cikakken katin shaida, yayin da wanda zai saya sai ya bayyana dalilin da ya sa yake son sayen ruwan batir din.

Haka kuma sai an kai rahoton cinikin wajen 'yan sanda.

Kotun ta kuma umarci gwamnatocin jiha su biya diyyar dalar amurka kusan 5,000, ga wadanda aka watsa wa ruwan batir domin kula da su.

Masu fafutuka dai sun yi maraba da wannan hukunci.

Akalla a kan samu hari da ruwan batir sau kusan dubu daya a duk shekara, wanda ake kaiwa mutane kuma mafi yawansu mata ne a Indiya.

Musamman matan da suka bijirewa samarinsu ko mazajensu ko kuma wadanda suka dauke su aiki.