Ana bikin cikar Mandela shekaru 95

Mista Nelson Mandela
Image caption Mandela na kwance a wani asibitin dake Pretoria, inda yake fama da cutar huhu

Al'ummar kasar Afrika ta Kudu za su gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban kasar bakin fata na farko, Nelson Mandela wanda ya cika shekaru 95 a duniya.

Mr. Mandela a halin yanzu yana kwance a asibiti rai kwa-kwai mutu kwa-kwai, inda yake fama da cutar huhu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar Mandela, don gudummawar da ya bayar kan wanzar da zaman lafiya da sasantawa.

An dai karfafawa mutanen kasar gwiwar su sadaukar da mintoci 67 domin yin wani aikin sa kai, duk dai a wani bangare na tunawa da shekaru sittin da biyar, da Mandela ya kwashe yana ayyukan ci gaban al'umma.

Tsohon shugaban Afrika ta Kudun ya shafe tsawon makonni shida a gadon asibiti yana jinya, sai dai 'yar sa Zindzi ta ce lafiyarsa na inganta.