Martani ga hukuncin da aka yankewa Navalny

Navalny a Kotu
Image caption Ana zargin Navalny ne da aikata rashawa

Kasashen duniya sun soki lamarin hukuncin daurin shekaru biyar da wata kotu a Rasha ta yankewa dan adawa nan Alexei Navalny.

Kotun ta sami Mr Navalny ne da laifin aikata rashawa a karshen shariar da ya ce tana da nasaba da siyasa.

Jakadan Amurka a Mosko, ya nuna rashin jin dadinsa da hukuncin.

Ita kuwa kungiyar Tarayyar Turai, cewa ta yi hukuncin ya saka alamar tambaya a kan ingancin tsarin shariar da ake amfani da shi a Rasha.

Wani kakakin gwamnatin Jamus ya bayyana shariar da cewa an yi ta ne kawai don duniya ta sani.

Shaidu sun ce jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar nuna goyon bayan ga Mr Navalny a birnin Mosko, kuma tuni jam'ian tsaron suka killace kowane dandanli na birnin ciki har da na Red Square.

Mr Navalny dai shi ne dan adawa na baya bayan a cikin jerin fitattun 'yan adawa da za a yanke wa hukuncin zama a gidan yari kuma mutum ne dake fafitukar yaki da rashawa.

Karin bayani