Australia za ta tasa keyar masu neman mafaka

Image caption Pirayi Minista, Kevin Rudd

Pirayi Ministan Australia Kevin Rudd, ya ce daga yanzu gwamnatinsa za ta daina baiwa masu neman mafaka dake isa kasar ta jirgin ruwa, izinin zama a kasar.

Yayinda yake bayyana sabuwar manufarsa kan batun shigi da fice gabannin babban zaben da zaa yi a kasar, Mista Rudd ya ce Australia ta cimma wata 'yarjejeniya ta shekara daya da gwamnatin tsibirin Papua New Guinea, domin duba bukatun masu neman mafakar:

"Masu neman mafakar da aka tura tsibirin Christmas, zaa kai su Manus ne da sauran yankuna na Papua New Guinea inda zaa duba bukatunsu", Kevin Ruud ya bayyana.

Mista Ruud ya kara da cewar wadanda ke bukatar mafaka a zahiri, za a kyale su su zauna a tsibirin na Papua New Guinea , amma wadanda ba a amince da bukatunsu ba, za a tasa keyarsu gida ko kuma zuwa wata kasar ta dabam.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama sun soki lamarin sabon shirin.

Karin bayani