Jigon 'yan adawar Cambodia ya dawo kasar

Image caption Sam Rainsy dai bai da iznin tsayawa takara a halin yanzu

Daya daga cikin jagororin 'yan adawa a cambodia Sam Rainsy ya dawo kasar, bayan shafe fiye da shekaru hudu yana gudun hijira.

Ya samu gagarumin tarbo daga magoya bayansa a filin saukar jiragen sama na birnin Phnom Penh.

Ya bar Cambodia ne saboda laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa, wadanda suka hada da zana wata taswirar iyakar kasar da Vietnam wadda ba daidai ba.

Sai dai ya musanta hakan ya na mai cewa abu ne da aka yi bisa dalilan siyasa.

An yankewa Mr Rainsy hukuncin dauri mai tsawo a shekarar 2010 duk da cewar baya kasar a lokacin, sai dai kotu ta yi masa afuwa a makon da ya gabata.

Amurka ta bukaci gwamnatin Firayin Minista Hun Sen da ta kyale shi ya shiga ayi da shi a zaben kasar wanda za a gudanar a karshen watan nan.

Sai dai har yanzu yana da haramcin tsayawa takarar kowane mukami.

Karin bayani