Za a mika wa gwamnatocin jihohi makarantun allo

Image caption 'Yan makarantar allo

Gwamnatin Najeriya ta ce a watan Agusta sallah za ta mika makarantun da ta gina don ilmantar almajirai masu karatun allo guda tamanin ga gwamnatocin jihohi.

Wannan dai wani bangare ne, na makarantu 125 da gwamnatin ta gina a wani yunkuri na rage yawan yaran da ba sa karatun boko a kasar.

Minista a ma'aikatar ilimi ta Najeriya, Mista Nyesom Wike, shi ne ya shaidawa manema labarai cewa makwanni biyu bayan salla za a mika wadanannan makarantu guda tamanin ga gwamnatocin jihohi.

Da ya ke karin bayani a kan Shirin Gwamnati na Ilimantar da almajirai, ministan ya ce yayin taron majalisar tattalin arziki ta kasa a yanke shawarar mika makarantun, wadanda ake sa ran za su fara daukar dalibai nan take don su fara karatu a shekarar karatu ta badi, wacce za ta fara a watan Satumba.

Karin bayani