'Isra'ila, Falasdinawa sun amince su yi sulhu'

John Kerry
Image caption John Kerry ya yabawa duka shugabanin Isra'ila da Falasdinwa kan 'nuna dattako'

Sakataren harkokin Wajen Amurka, John Kerry, yace Isra'ila da Falasdinawa sun amince su maido da tattaunawar kawo zaman lafiya ta ido da ido a karon farko cikin shekaru uku.

Yace za a soma tattaunawar farko ne a Washington nan da mako daya amma bai bayarda karin bayani ba kan yarjejeniyar.

Sai dai Ministar shara'a ta Israila, Tzipi Livni wadda ita ce zata wakilce ta wajen tattaunawar tace sasantawar za ta yi wuya.

Shi ma Wasel yousuf, wani babban jigon a hukumar mulkin falasdinawa ta PLO yace wannan sanarwar ba tana nufin a koma kan teburin tattaunawa ba.

Haka ma kungiyar Hamas wadda ke mulkin zirin Gaza tace shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas baya da 'yancin shiga tattaunawar sulhu a madadin al'ummar Falasdinu.

Karin bayani