'Yan Mali na bukatar tallafin abinci

Image caption Mutane miliyon daya ke bukatar abinci a Mali

Kungiyar bada agaji ta musulunci dake Birtaniya tayi kashedin cewa, duk da cewar, an kawo karshen yaki a Mali, 'yan kasar da dama suna fuskantar matsalolin rayuwa.

Kungiyar bada agajin ta Islamic Relief tace, duk da cewar, dakarun Faransa da na kasashen Afirka sun kawar da 'yan tawaye daga arewacin kasar, amma har yanzu makarantu da dama a rufe suke, kuma kasuwanni da dama ma a rufe suke.

Islamic Relief ta ce a yanzu haka mutane kusan miliyon daya da rabi, sun dogara ne kacokan a tallafin abincin da ake kai musu, a yayinda wasu karin mutane miliyon biyu ke fuskantar hadarin matsanninci yunwa.

Tun kafin sojojin Faranci su jagoranci kawarda mayaka 'yan gwagwarmayar Islama, kusan kashi tamanin cikin dari na abincin da ake ci a arewacin Mali, ana samunsa ne daga kudancin kasar ko kuma makwabtan kasashe kamar Algeria da Libya.

Karin bayani