Satar danyen mai na damuwar Najeriya

Image caption Yankin Niger Delta shi ne yafi ko wane arzikin mai a yammacin Africa.

Majalisar tattalin arzikin Najeriya ta nuna damuwa dangane da yawaitar matsalar satar danyen mai a yankin Niger-Delta.

Majalisar ta ce gwamnati na asarar a kalla gangar mai 400,000 a kowace rana lamarin da ke haifar da gibi ga kudin shigarda take samu.

Don haka ne majalisar ta bukaci a rika hukunta duk wanda aka kama da laifin satar man.

Sai dai ana ganin da wuya gwamnatin kasar ta iya hukunta wadanda ake zargi da satar danyen man ko da an same su da laifi saboda karfin fada aji da kuma kusacinda suke da shi gareta.

Karin bayani