Obama ya bukaci sansanta Isra'ila da Falasdinawa

Barack Obama
Image caption Barack Obama na son ganin karshen rikicin Gabas ta Tsakiya

Shugaba Barack Obama yayi kira ga kasar Isra'ila da ta koma kan teburin sulhu da Falasdinawa ba da wani bata lokaci ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Sakataren harkokin wajen Amurkar John Kerry ke ziyartar yankin Gabar ta Tsakiya a wani yunkuri na sake farfado da tattaunawar sulhunda ta cije.

John Kerry dai ya tsawaita kasancewarsa a yankin gabas ta Tsakiya ne da fatan samun ci-gaba a tattaunawar kawo zaman lafiya.

A yayinda yake a can, shi kuma shugaban na Amurka ya kira Firayin ministan Isra'ilan Benyamin Natanyahu ne ta wayar tarho domin kara baiwa kokarin da Kerry ke yi kwarin gwiwa.

Sanarwar White House

A cewar wata sanarwa da fadar White House ta fitar, tattaunawar da shugabanin biyu suka yi irin wadda suka saba yi ce; amma ta kasance dama mai kyau ga Shugaban na Amurka ta yin kira ga Fariyin Minista Natanyahu na ya koma kan teburin sulhu da falasdinawa ba tare da wani bata lokaci ba.

Amma kuma abu ne mai wuya ace an samu ci-gaba na azo-a-gani a lokacin wannan ziyara-inji wakiliyar BBC a Washington.

Saboda manyan shuagabannin falasdinawa sun yi wani taro a ranar alhamis kan batun, amma suka watse ba tare da yanke wata shawara ba. Ana dai saran Sakataren na Amurka ya sake ganawa da shugabannin Isra'ila da Falasdinawan yau jumu'a kafin ya kama hanyarsa ta komawa Amurka.

Karin bayani