Ni ma da an kashe ni kamar Trayvon Martin- Obama

Image caption Shugaba Barack Obama ya damu da yadda aka wanke Zimmerman daga laifi

Shugaba Barack Obama yace shi ma da ya shiga irin halinda Trayvon Martin ya shiga, shekaru 35 da suka wuce; a cikin kalamansa na farko kan hukuncinda aka yankewa Zimmerman a makon jiya.

An dai harbe Trayvon dan shekaru 17, wanda bakar fata ne har lahira a jahar Florida cikin watan Febrairun 2012.

Wanda ya kashe shi Geoge Zimmerman mai shekaru 29, yace ya bude wa dan saurayin wanda bai rike da kowane makami wuta ne domin kare kansa; kuma wata kotu a Floridan ta wanke shi daga laifin aikata kisan kai.

A yayin wani taron 'yan jarida na ba-zata, Mr. Obama yace bakaken fata 'yan kalilan ne ba a nunawa bambancin launin fata ba a Amurka.

Karin bayani