Amurka ta shigarda kara kan Belmokhtar

Image caption Mokhtar Belmokhtar dai ya rasa idonsa daya ne garin fada da sojan Aljeriya a shekara 1990.

Masu shigarda kara a Amurka sun tuhumi tsohon shugaban kungiyar Al-ka'ida a yankin Maghrib, Mokhtar Belmokhtar, dangane harinda aka kaiwa wata masana'atar sarrafa gas dake kasar Aljeriya a watan Janairu.

Lamarin dai yayi sanadiyyar mutuwar mutane 37 ciki har da Amurkawa uku.

Ana tuhumarsa ne da satar mutane, da yin garkuwa da su da kuma hada baki domin a yi amfani da makamin kare dangi.

Har yanzu dai ba a san inda Belmokhtar din yake ba.

Sojan Aljeriya ne dai suka kawo karshen kawanyarda aka yiwa masana'antar da kai wani farmaki. Amma sai da mayaka 29 da ma'aikata 'yan kasashen waje 37 suka mutu.

Karin bayani