An rantsar da Sarki Phillipe na Belgium

Image caption Sarki Phillipe da mahaifinsa tsohon sarki Albert

An rantsar da sabon Sarkin Belgium, Sarki Philippe a harabar ginin majalisar dokoki a Brussels a matsayin Sarki na bakwai a jerin sarakunan kasar.

Sarki Philippe ya gaji mahaifinsa Sarki Albert wanda ya yi murabus saboda tsufa da rashin koshin lafiya.

Sarki Albert bayan shafe shekaru 20 yana jan ragamar masarautar Belgium, daga yau, ya ja gefe inda dansa zai cigaba da mulkin.

'Yan majalisar sun yi ta tafi bayan da Sarkin ya yi alkawarin bin dokoki da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda ya furta cikin harsuna uku da ake amfani da su a kasar a hukumance wadanda suka kunshi Dutch da Faransaci da kuma Jamusanci.

Sai dai kuma jam'iyyar 'yan aware ta kauracewa bukin a wani matakin nuna adawa, a yayinda ita kuma babbar jam'iyyar adawa wato New Flemish Alliance ta tura tawagar mutane kadan wajen bukin.

Karin bayani