Assad mamugunci ne- Cameron

Image caption David Cameron na Birtaniya

Firayi ministan Birtaniya David Cameron ya shaidawa BBC cewa shugaban Siriya Bashar al-Assad na samun karin karfi yayin da yake kokarin kawar da boren da ake masa tsawon shekaru biyu.

Ya baiyana Assad a matsayin mamugunci, ya kara da cewa yanayin da ake ciki yanzu ya ci tura.

Cameron yace "mai yiwuwa ya kara yin karfi fiye da yadda yake yan watannin da suka wuce".

"Babu shakka akwai matsala tattare da wani bangare na yan tawaye wadanda suka kasance masu tsanani, amma abin da ya kamata mu yi shine hada hannu da aminanmu na kasa da kasa domin taimakawa miliyoyin 'yan Siriya wadanda ke bukatar 'yanci da wanzuwar dimokradiya a Siriya", Mista Cameron ya jaddada.