Jam'iyyar Shinzo Abe na kan gaba a Japan

Image caption Wata tsohuwa na kada kuri'a a Japan

Sakamakon farko na zaben majalisar dattijai a Japan ya nuna gagarumar nasara ga gwamnatin hadin gwiwa ta Firaminista Shinzo Abe.

Idan sakamakon ya tabbata Mr Abe zai kasance yana da cikakken rinjaye a majalisun dokokin kasar guda biyu.

Sakamakon dai zai baiwa Firaministan kwarin giwar aiwatar da garanbawul wanda ya yi imanin sun zama wajibi domin ci gaba da farfado da tattalin arzikin kasar daga yanayin da ya shiga.

Tsawon watanni shida da suka wuce, Mista Abe ya samu nasarar sake farfado da tattalin arzikin kasar da ya fuskanci koma baya shekaru ashirin da suka wuce.

Karin bayani