'An haramtawa mata zuwa kasuwa su kadai'

Image caption Wasu mata a Pakistan

Malaman musulunci da shugabannin al'umma a arewa maso yammacin Pakistan sun haramtawa mata zuwa kasuwa su kadai domin yin siyayya ba tare da rakiyar wani dan uwansu namiji ba.

Wani babban malamin musulunci a lardin Khyber Pakhtunkhwa ya ce matan dake tafiya kasuwa suna yada dabi'a mara kyau musamman a watan Ramadan.

Rahotanni daga yankin sun ce malaman sun bukaci 'yan sanda su karfafa haramcin amma 'yan sandan sun ki.

Sun kuma yi kira ga masu kantuna kada su sayar da kaya ga duk matar da bata da dan rakiya.

Yawancin mata a yankin arewa maso yammacin Pakistan suna lullubi su suturce jikinsu suna kuma zaman kulle ne a gida.

Karin bayani