An yi zanga-zanga a birane 100 na Amurka

Image caption Bakaken fata sun soki matakin kotun

An gudanar da zanga zanga a birane fiye da dari daya na kasar Amirka domin nuna damuwa da hukuncin kotu da ta wanke Goerge Zimmerman wanda ya harbe wani yaro matashi bakar fata Trayvon Martin a Jihar Florida a watan Fabrairun shekarar da ta gabata.

Hukuncin ya haifar da sabuwar muhawara mai fadi a game da mallakar bindiga da wariyar jinsi da kuma dokoki da suka shafi kare kai.

Mahaifiyar Trayvon Martin Sybrina Fulton da take jawabi a wajen wani gangami a New York ta ce tana son nuna jagoranci abin misali tana mai kiran daukar matakai na lumana domin sauya wadannan dokoki.

Wani dan gwagwarmayar kare hakkin bil Adama Reverend Al Sharpton wanda ya jagoranci shirya gangamin ya ce ba za su daina ba har sai an sauya wasu dokoki.

Karin bayani