Ana zaben majalisar dokoki a Japan

Wata mata na kada kuri'a a kasar Japan
Image caption Wata mata na kada kuri'a a kasar Japan

Masu kada kuri'a a Japan na zaben majalisar dokoki, da ake hasashen jam'iyyar Liberal Democratic Party za ta sake samun nasarar rike iko.

Jam'iyyar za ta samu rinjaye a dukkan majalisun wakilan kasar a karon farko tun shekara ta dubu biyu da bakwai.

Haka nan kuma zai kara baiwa Prime Minista Shinzo Abe kwarin-gwiwa, bayan komawar sa kan kujerar mulki a watan Disambar da ya wuce.

Ya dai yi alwashin fitar da kasar ta Japan daga tsaikon da take fuskanta na tattalin arziki tun kimanin shekaru 20 da suka gabata.

Idan har jam'iyyar ta Mr Abe ta samu nasara, zai samu damar aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki masu tsanani, wadanda ba su da farin jini a wurin 'yan kasar.