Matar Yarima William na kan gwiwa

Kate Middleton
Image caption Birtaniya na jiran tsammanin Da ko 'Yar da Duchess ta Cambridge za ta haifa, wanda zai zamo mai jiran gadon sarauta na uku

An kai Duchess ta Cambridge Catherine wani asibiti yayin da ta fara nakuda, a cewar fadar Kesington.

An dai dauke ta ne a mota daga fada zuwa asibitin St. Mary dake Paddington a yammacin London, tare da mijinta Duke na Cambridge.

Kawo yanzu dai ma'auratan ba su san mace ko namiji za ta haifa ba, wanda zai zamo na uku mai jiran gadon sarautar Birtaniya.

"Komai yana tafiya lami lafiya." A cewar kakakin fadar, abu na gaba zai zamo sanarwar haihuwar.

Manema labarai na duniya sun kafa sansani a wajen asibitin na St. Mary, inda suka kwashe kwanaki suna jiran labarin haihuwar.

A hukumance dai ba a sanar da ainihin ranar da Kate za ta haihu ba, sai dai da dama an fi sa ran a tsakiyar watan Yulin da muke ciki.

An ga jerin motocin gidan sarauta a kofar shiga asibitin ta baya, da misalin karfe shida na safe agogon Birtaniya, yayin da sai bayan sa'a guda da rabi ne kuma, fadar ta fitar da sanarwar cewa Duchess din na kan gwiwa.

Tawagar manyan likitoci ne ke kula da mai nakudar, inda tsohon mai kula da lafiyar sarauniya, Marcus Setchell ke jagorantarsu.