An samu munanan girgizar kasa a China

Gingizar kasa a China
Image caption Tawirar girgizar kasa a China

An samu munanan girgizar kasa guda biyu a lardin Gansu, dake arewa maso yammacin kasar Sin, abin da ya hallaka mutane 75, yayin da wasu sama da 400 suka jikkata.

Zirgizar kasar ta farko da aka samu a kusa da birnin Dingxi na da karfin maki biyar da digo 98, yayin da zurfinta ya kai kilomita tara da digo takwas, a cewar wani binciken yanayin kasa na Amurka.

Sa'a guda bayan nan ne kuma aka sake samun wata girgizar kasar mai karfin maki biyar da digo shida a gurin.

A shekarar 2008 an taba samun girgizar kasa a lardin Sichuan, wanda ya kai ga mutuwar mutane dubu 90, yayin da miliyoyi kuma suka rasa matsugunansu.