A budewa 'yan tawaye wuta- Shugaba Santos

'Yan tawayen kungiyar Farc a kasar Colombia
Image caption 'Yan tawayen kungiyar Farc a kasar Colombia

Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos ya ce ya umurci sojoji su cigaba da bude wuta har sai an kawo karshen tawaye na kungiyar FARC.

Kalaman na shi na bacin rai sun zo ne bayan an kashe sojoji goma sha-biyar, a wani harin kwanton-bauna da aka kai musu a yankin Arauca dake kusa da kan iyakar Venezuela.

Sojojin sun ce sun kame wasu 'yan kungiyar tawayen ta FARC dangane da wannan hari da aka kai.

Shugaba Santos din ya ce 'yan tawayen basu da wani karfi ko na gamin gafara da zai kai su ga samun galaba.

A yanzu haka dai gwamnatin ta Colombia da kungiyar tawayen masu neman sauyi suna shawarwarin sulhu a kasar Cuba, domin kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru hamsin ana yi.

'Yan tawayen sun yi kiran tsagaita wuta a lokacin shawarwarin baya, amma kuma gwamnatin ta ce wannan abu ne kawai da zai baiwa 'yan kungiyar ta FARC damar sake hadewa da tara makamai.