EU ta saka Hezbollah a jerin 'yan ta'adda

Image caption Mayakan kungiyar Hezbollah

Ministocin harkokin wajen kasashen Tarayya Turai, sun yake hukuncin saka bangaren soja na kungiyar masu fafutuka ta Hebollah a jerin kungiyoyin ta'addanci, abun da ke nufin cewa yanzu tara kudaden domin taimakawa kungiyar, haramun ne a Turai.

Ministocin sun kafa hujja da harin da ake zargin kungiyar ta Hebollah ta kai a bara a Bulgaria ne a kan wasu 'yan Isra'ila dake yawon bude ido, wajen yanke hukuncin nasu .

Jami'an diplomasiyya sun cimma wanna matsayarce bayan da duka wakilai 28 suka amince a Brussels.

Ministan harkokin Jamus, Guido Westerwelle ya ce Turai ba za ta kawar da kai daga ta'adanci ba.

Karin bayani