Zaman dar-dar a birnin Kidal na Mali

Wasu mutane na kona tayoyi a Kidal
Image caption A farkon watan Yuli ne dai wasu mutane suka kona tayoyi a Kidal domin adawa da shigan sojoji birnin

Mako daya kafin babban zaben shugaban kasa a Mali, an shiga zaman dar-dar a birnin Kidal.

Hakan ya biyo bayan gano wani bam a wata kasuwa, yayin da kuma aka sako wasu jami'an zabe hudu da mataimakin magajin garin da wasu 'yan bindiga suka sace.

Ana cigaba da nuna fargaba game da matsalar tsaron da wasu ke ganin ka iya kiwa ga rashin kwanciyar hankali bayan zabe.

A makon jiya ne dai shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arziki kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ko CEDEAO, suka bukaci taimakon dalar Amurka miliya 25, domin cike gibin ayyukan zabe a Mali.

Abin da wasu masu sharhi su ka yi nuni da cewa ba a shirya wa zaben na Mali ba.

Ko da yake shugaban kungiyar ta ECOWAS ya ce fatattakar da dakaru karkashin jagorancin Faransa suka yi, ya kawo nutsuwa da kwanciyar hankali a arewacin Malin.