'Yar Morsi ta zargi sojoji da sace mahaifinta

Image caption 'Ya'yan Muhammed Morsi

'Yar hambararen shugaban Masar, Mohammed Morsi, ta zargi rundinar sojojin kasar da sace mahaifinta.

A sanarwar farko da iyalan Mr Morsi din suka fitar tun bayan da sojoji suka sauke shi farkon wannan watan, Shaimaa Morsi ta fadawa manema labarai a birnin Alkahira cewa sun dora alhakin duk abun da ya faru da lafiyar mahaifinsu a kan shugaban rundinar sojin Masar, Janar Abdel Fatah al Sisi.

Ta ce iyalansa za su shigar da kara a gaban kotun duniya mai hukunta manyan laifufuka ta ICC, domin kaddamar da bincike kan abun da ta kira juyin mulkin da aka zubar da jini.

Karin bayani