An gano gawarwakin mata uku a Ohio

Birnin Cleveland, jihar Ohio a Amurka
Image caption Birnin Cleveland, jihar Ohio a Amurka

'Yansanda na gudanar da bincike a birnin Cleveland na Amurka, bayan gano gawarwakin mata uku da aka kunshe cikin wasu jikkunan leda.

Wani mutum da aka yi zargi wanda sunan sa yana cikin rajistar masu cin zarafin mata yanzu haka na hannun 'yan sanda.

Hukumomi sun ce, an kashe matan ne cikin kwanaki goma da suka gabata.

Tun farko dai wani babban jami'in 'yansanda ya yi gargadin cewa mai yiwuwa a kara samun mutanen da aka kashe.

An dai samu gawarwakin matan ne a wurare daban-daban dake kusa da juna, a unguwar marasa galihu dake da kwangayen gidaje da dama.

Magajin garin gabashin birnin Clevland Gary Norton, ya ce wanda ake zargin mai kimanin shekaru 35 na hannun 'yansanda.

Ya kuma yi nuni da cewa akwai yiwuwar samun karin wasu gawarwakin.

Wani kwamandan 'yansanda dake yankin Ralp Spotts ya ce, za a yi taka tsan-tsan wajen gudanar da binciken.

Wannan dai shine laifi na uku mafi girma da ya shafi mata na baya bayan nan da aka taba samu a birnin Cleveland.

A shekaru biyun da suka gabata ne aka yankewa wani mai kisan dauki daidai Anthony Sowell hukuncin kisa, bayan da aka same shi da aikata laifin kisan wasu mata goma sha daya.

A watan Mayun wannan shekarar aka samu wasu mata uku da ransu a kullle a wani gida, shekaru sama da goma bayan bacewarsu.