Bincike na nuna cewa akwai mai a jihar Naija

Wani kampanin mai a Nijeriya
Image caption Wani kampanin mai a Nijeriya

Yayinda ake ci gaba da muhawara kan batun da ya shafi arzikin man petur a Nijeriya, inda yankuna dake da arzikin ke bugun kirjin cewa da bazarsu sauran yankuna ke rawa, bisa dukkan alamu wasu jihohin arewacin Nijeriyar na daukar matakan ganin an daina yi masu kallon ci-ma-zaune.

Yanzu haka wani kwaryakwaryar sakamakon bincike da aka fitar a kan tafkin Bida , a jihar Naija ya nuna cewa adadin man fetur da kuma iskar gas dake cikin tafkin zai iya zarta na yankin Niger Delta.

Gwamnatin jihar ta Niger ce ta kafa kwamitin, kuma ya ce zai hada karfi da wasu jihohin arewacin Nijeriya domin aikin gano man petur din .