An tuhumi wani da kashe dattijo musulmi a Birtaniya

Marigayi Mohammed Saleem
Image caption Marigayi Mohammed Saleem

'Yan sandan Burtaniya sun tuhumi wani dalibi dan Ukraine da laifin kisan wani dattijo Musulmi a Birmingham.

'Yan sanda sun ce kisan yana da alaka da ta'addanci.

An dabawa Mohammed Saleem mai shekaru 75, wuka a cikin watan Afrilu ne, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa gida daga masallaci bayan sallar Isha.

Gobe ,Talata ne aka shirya wanda ake zargin, Pavlo Lapshyn zai gurfana a kotu.

Har illa yau, 'Yan sanda sun ce suna yi ma shi tambayoyi game da wasu hare-haren bam da aka kai kusa da wasu masallatai a garuruwan Walsall, da Tipton da kuma Wolverhampton, dukkansu a Ingila.