An kashe mutane 9 a tashin hankalin Masar

Zanga-zangar magoya bayan Mohammed Morsi
Image caption Zanga-zangar magoya bayan Mohammed Morsi

Akalla mutane tara aka kashe a wasu arangamar da suka faru a cikin dare, tsakanin magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi da kuma masu adawa da shi, a cewar jami'ai.

Wasu daga cikin tashin hankalin sun faru ne a wajen da masu goyon bayan Mr. Morsi ke zaman durshen.

Iyalan Morsi dai sun zargi sojoji da sace shi.

Ana dai cigaba da tsare tsohon shugaban kasar a wani gurin da ba a bayyana ba, kuma ba tare da an tuhume shi ba.

Yana dai tsare ne tun lokacin da hafsan sojin kasar, janar Abdul Fattah al-Sisi ya sanar da tumbuke shi a ranar 3 ga watan Yuli.

Kungiyar 'yan uwa musulmi ta ki amince wa da sabuwar gwamnatin rikon kwaryar dake da goyon bayan sojoji.

Inda magoya bayan kungiyar suka cigaba da yin zanga-zanga a kan tituna kullum.

Rikicin da ya biyo bayan tumbuke Mr. Morsi ya yi sanadiyyar rayukan akalla mutane 60.