Ana farautar fursunonin da suka tsere a Iraki

Gidan yarin Abu Ghraib a Iraki
Image caption Gidan yarin Abu Ghraib a Iraki

Jami'an tsaro a Iraki na can na farautar daruruwan fursunonin da suka tsere, bayan wasu hare hare da mayakan wata kungiya mai alaka da ta alQaeda suka tsara suka kuma kai a lokaci guda kan manyan gidajen yarin kasar biyu.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na ma'aikatar cikingida na cewa maharan sun bude wuta da makaman iggwa a kan gidan yarin Abu Ghraib da kuma Taji, lokacin da fursunonin ke bore. Sanarwar ta ce jami'an tsaro sun kashe wasu daga cikin maharan.

Gwamnatin Irakin na cewa 'yan bindigar sun samu taimako ne daga wasu gandirebobi.

A daya daga cikin gidajen yarin, na Abu Ghraib ne ake tsare da wasu kusoshin kungiyar alqaeda na kasar