Rahoto kan filayen noma a Afrika

World Bank
Image caption World Bank

Babban Bankin Duniya ya ce al'ummar Afrika za su ci gajiyar bunkasar tattalin arzikin da nahiyar ke samu.

idan har manoma za su samu damar mallakar filayen noma.

Wani Sabon rahoton da bankin ya fitar na cewa, Afrika na da kusan rabin filin noma da ake da shi a duniya da ba a yin amfani da shi, nahiyar na da filin noma kadada milyan 200 da ba a nomawa.

Wannan adadi ya rubanya yawan filin noman da nahiyar Turai ke da shi baki daya sau biyar.

Rahoton ya kuma ce, an kasa amfani da dimbin filaye masu albarkar noma ne, saboda sarkakiyar dake tattare da mallakar gonaki.

Binciken ya yi nuni da cewa yadda ake tafiyar da lamuran filayen cike da kumbiya-kumbiya ne ke haddasa matsalar.

Kuma a yankunan karkara ana ma yin fada da rigingimu a kan mallakar filaye.

Mutane da dama sun fuskanci shari'u dake da nasaba da kokarin sayen filin noma a Afirka.

Galibin lokuta filaye a birane ana rarraba su, a kuma sake rarrabawa iyalai daga zamani zuwa zamani, abin da ke hadasa rudani a tsakanin masu filayen.

A yankunan karkara rikicin mallakar fili ko na kabilanci ya zama ruwan dare gama-duniya.

Rahoton dai ya nemi gwamnatoci da su daidaita lamura ga al'ummomi ko kuma daidaikun mutane masu filayen noma.

Karin bayani