Bikin bude Ranar Matasa ta Duniya a Brazil

  • 24 Yuli 2013
Bikin Ranar Matasa ta Duniya a kasar Brazil
Bikin Ranar Matasa ta Duniya a kasar Brazil

A kasar Brazil mutane dubu dari hudu ne suka hallara a bakin tekun Copa-cabana dake Rio de Janeiro, domin bikin bude Ranar Matasa ta Duniya.

Bikin na kasa da kasa na jan hankulan mabiya darikar Roman Katolika daga sassa dabam-dabam na duniya.

Fafaroma Francis na kasar ta Brazil don halartar bikin da zai yi ranar Alhamis.

Taron addu'oin a gabar teku, wata alamar fara shagulgulgulan da za a shafe mako guda ana yi ne.

Kafin fara wannan biki, dukkan layukkan jirage na karkashin kasa sun daina aiki saboda katsewar wutar lantarki.

Hakan kuwa ya dakatar da matafiya har na tsawon sama da sa'a guda.

Masu sa ido na kasa da kasa sun ce, wannan lamari ya haifar da damuwa game da batun ababan more rayuwa, yayin da kasar ke shirin karbar bakuncin gasar wasan kwallon kafa ta duniya, da na Olympics da za a gudanarwa cikin shekara ta 2016 a birnin Rio.