Al-Sisi ya yi kira a yi gangami a Masar

Janar  Abdul Fatah al-Sisi
Image caption Janar Abdul Fatah al-Sisi

Shugaban rundunar sojin Masar, Janar Abd-al- Fatah al-Sisi, ya yi kira ga jama'a da su yi zanga-zanga ranar Juma'a mai zuwa, domin nuna goyon baya ga kokarin hukumomin kasar na yaki da abin da ya kira, ta'addanci.

Al-Sisi ya furta hakan ne a wani bikin yaye sojojin da aka watsa ta gidan talabijin din kasar.

Janar al- Sisi ya nemi jama'a su ba shi iko tare da rundunar soji da kuma Hukumar 'yan sandan kasar, na tinkarar abubuwan da ya bayyana da cewa tada zaune tsaye ne, da kuma ta'addanci da kasar ke fuskanta.

Sai dai wani kusa a jam'iyyar 'Yan Uwa Musulmi ya ce kalaman na Janar al- Sisi, sun kasance wata barazana, kuma ba za su hana su cigaba da zanga-zangar nuna goyon baya ga hambararren shugaba Mohammed Morsi ba.

Mai aiko wa da BBC rahotanni daga Alkahira ya ce, kalaman na Al-Sisi na nuna wanda ke da iko a Masar, wato sojoji ne ba wai gwamnatin rikon kwarya ba.

Mutane biyu sun sake mutuwa a arangamar da aka yi a daren ranar Talata, bayan guda taran da suka rasa ransu a irin wannan tashin hankali a daren ranar Litinin a Alkahiran.