Najeriya da Kamaru za su yi taro kan ambaliyar ruwa

Taswirar yankin Bakasi, kan iyakar Najeriya da Kamaru
Image caption Taswirar yankin Bakasi, kan iyakar Najeriya da Kamaru

Jami'an gwamnatocin Najeriya da na Kamaru za su fara wani taron kwanaki ukku, don duba yadda za su kaucewa sake abkuwar ambaliyar ruwa.

Matsalar na faruwa ne sanadiyar sakin ruwa daga madatsar ruwan Lagdo da ke kasar Kamarun.

Yankuna da dama ne dai ambaliyar ruwan ta yi wa barna a jihohin Adamawa, da Benue da Taraba a bara.

A bana ma ana fargabar cewa gwamnatin Kamarun za ta sake bude madatsar ruwan, lamarin da a cewar mahukuntan Najeriyar zai iya haddasa asarar rayuka.