William da Kate sun rada ma dansu suna

Jaririn Kate da Yerima William
Image caption Jaririn Kate da Yerima William

Yerima William da mai dakinsa Kate sun radawa jaririnsu nan, George Alexander Louis

Jami'an fadar masarautar Birtaniya sun ce, za'a rika kiran jaririn Yerima, George na Cambridge.

Shi ne dai na uku a jerin masu jiran saurautar Birtaniya.

An dai haife shi ne ranar Litinin a asibitin St. Marys dake birnin London.

A yau Laraba ne Yerima William da Uwargidan tasa Duchess ta Cambridge suka yi kwanan farko a gidansu dake Fadar Kensington a London da dan nasu.

Tun farko, Kate da Yerima William sun fito rike da jaririn, inda suka nuna shi ga manema labarai da sauran jama'ar da suka yi dafifi a kofar asibitin kafin su wuce gida.