Kotu ta zargi Bo Xilai da laifin cin hanci

Image caption Kotu ta zargi Bo Xilai da laifin cin hanci

Wata kotu a Kasar Sin ta zargi tsohon dan siyasar nan Bo Xi Lai da laifin cin hanci da rashawa da kuma amfani da mukami ta hanyar da bata da ce ba.

Matakin da masu gabatar da kara suka dauka a gabashin birnin Jinan na tuhumar Mr. Bo, tsohon shugaban jam'iyyar Komunusanci, ya share hanyar gurfanar da shi a gaban shari'a.

An dai shafe fiye da shekara guda ba a ga Bo -Xi Lai a bainar jama'a ba, bayan kunyata shi da aka yi sakamakon wani rikicin siyasa da ya kunno kai a cikin jam'iyyarsa ta Komunis.

A bara ne aka yankewa mai dakinsa hukuncin daurin gidan yari, saboda samunta da laifin kisan wani abokin huldar kasuwancinta kuma dan Kasar Birtaniya, Neil Heywood.

Karin bayani