An sace shanu 2000 a jihar plato

Garken shanu
Image caption Matsalar satar shanu na faruwa a wasu kasashen nahiyar Afrika

Kimanin shanu dubu biyu aka sace tare da harbe wasu daga cikinsu a karamar hukumar Wase dake jihar plato a Najeriya.

Satar shanu na daga cikin matsalolin dake janyo rikicin kabilancin da ya-ki-ci yaki-cinye wa a jihar dake tsakiyar Najeriyar.

Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ake yin wani taron sasantawa da kabilu daban-daban na yankin.

Fiye da shanu 500 ne dai aka sace, a lokacin irin wannan taron sasantawar a Shendam, a ranar Litinin din data gabata.

Shanu na da daraja sosai a rayuwar Fulani, inda a mafi yawancin lokuta rayuwarsu ta kan dogara da dabbobin.