An karbe ayyukan majalisar Jihar Rivers

Majalisar Dattawa a Najeriya ta bi sahun Majalisar Wakilai ta kasar wajen zartar da wani kudiri na karbar ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Rivers dake fama da rikici.

Makwanni biyu da suka wuce ne Majalisar Wakilan ta zartar da irin wannan kudirin, yayinda Majalisar Dattawan a nata bangaren ta kafa wani kwamiti don ya binciki lamarin kafin ta kai ga fadar matsayinta.

'Yan Majalisar Dattawan sun zartar da wannan kudirin ne bayan da kwamitin data kafa ya yi tattaki har zuwa jihar ta Rivers kafin ya gabatar mata da shawarwarinsa.

Kwamitin ya ce amincewa da sharwarin wajibi ne, idan dai ana son a shawo kan matsalar da ta addabi jihar.

Majalisar Dokokin Jihar Rivers din dai ta rabu gida biyu tsakanin maso goyon bayan Gwamna Rotimi Amaechi da masu adawa da shi.

Shi dai gwamnan ya na sa-in-sa da Shugaba Goodluck Jonathan ne, sa-in-san da ake ganin cewa na da alaka da batun zaben shekara ta 2015, inda ake rade radin cewa Shugaba Jonathan na son sake yin takara.

Shi kuwa Gwamnan Amaechin ana zargin cewa yana son yin takarar neman mataimakin shugaban kasa ne a karkashin wani dan takara daga arewacin kasar -- zargin da ya musunta.

Shugaba Jonathan da Gwamna Amaechin duk sun fito daga shiyya daya ne.

Karin bayani