Halliburton ya amince da laifin malalar mai

Image caption Halliburton ya amince da laifin malalar mai a gabar tekun Mexico

Daya daga cikin manyan bangarorin da suka samu kansu cikin bala'in malalar mai a gabar tekun Mexico a shekarar 2010 Halliburton Energy Services, ya amince ya amsa laifinsa na hujjar yin ta'adi da ya yi.

Sashen shari'a na Kasar Amurka ya ce kamfanin Halliburton ya kuma amince ya biya wata tara idan har kotu ta amince da hakan, sannan ya cigaba da aiki tare da binciken da gwamnatin Amurka ke yi.

Wasu kamfanoni biyu da abin ya shafa na BP da Transco-cean tuni suka amince da cewar sun yi ba daidai ba.

Mutane goma sha daya ne suka mutu a lokacin da wata rijiyar mai ta fashe.

Karin bayani