Akalla mutane 40 sun mutu a Iraqi

Image caption Akalla mutane 40 sun mutu a harin bama-bamai a Iraqi

An bayar da rahotan cewa akalla mutane arba'in ne aka kashe a wasu jerin bama bamai da suka fashe da kuma harbe harbe a Iraqi.

A daya daga cikin abubuwan da suka auku mafi muni, mutane goma sha biyar ne suka mutu a harin bom da aka kai a Nawfil.

A wasu wuraren kuma, 'yan bindiga sun kai hari a sansanin soji domin su kawar da hankalin jami'an tsaro.

Haka kuma sun datse hanyar kusa da garin Sulaiman Bek, inda suka rinka dakatar da ababan hawa, suka harbe direbobi goma sha hudu, dukkaninsu 'yan Shi'a.

Wannan lamura dai sun auku ne a arewacin birnin Bagdad.

Masu aiko da rahotanni sunce kashe-kashen bangarori a Iraqi, na nuni da yadda harkar tsaro ta tabarbare.

Karin bayani