An kamalla yakin neman zabe a Mali

Image caption Hotunan 'yan takara a Mali

A yau (Juma'a) ne aka kammala yakin neman zabe a kasar Mali gabannin zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.

Yawancin 'yan takarar tsofaffin Ministocin kasar ne wadanda suka hada da Soumaila Cisse wanda ake dauka a matsayin daya daga cikin yan takarar da ke sahun gaba tare da Dramane Dembele wanda yake sabon shiga a harkar siyasar Mali.

Za dai a gudanar da zaben ne bayan shafe tsawon lokaci ana tashin hankali a kasar.

An dai hambarar da gwamnatin shugaba Amadou Toure a watan Maris din shekarar da ta gabata daga bisani kuma masu kaifin kishin islama suka kwace iko da arewacin kasar.

A cikin wannan shekarar dakarun sojin Fransa suka fatattaki yan tawayen sai dai har yanzu ana cigaba da rikici a kaar ta Mali.