Ban Ki Moon ya yi kira a saki Morsi

Image caption Ana zazzafar Zanga-zanga a Masar

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya yi kira ga sojin Kasar Masar dasu saki tsohon Shugaban Kasar Mohammed Morsi da sauran shugabannin 'yan uwa musulmi da suka tsare a cikin Kasar.

Kalamansa na zuwa ne yayin da magoya baya da kuma masu adawa da Mr Morsi ke gudanar da gagarumin gangami a daukacin fadin Kasar.

Jagoran 'yan uwa musulmi Mohammed Badie, ya ce sojoji sun aikata mummunan laifin da ya zarta lalata daki mai tsarki na Ka'aba a birnin Makka, ta hanyar hanbarar da zababben Shugaban Kasar.

Rundunar sojin Kasar dai ta sake yin kira ga jama'a dasu fito kan tituna domin yin fito na fito da abin da suka bayyana a matsayin ta'addanci.

Karin bayani