Zanga-zanga ta zafafa a Tunisia

Image caption Zanga-zanga ta zafafa a Tunisia kan kisan Brahmi

Zanga-zangar ta kunno kai ne bayan kisan da aka yiwa wani jagoran 'yan adawa na Kasar Mohammed Brahmi.

An dai cinnawa hedikwatar jam'iyyar Ennahada wuta dake garin Sidi Bouzid.

Sai dai shugaban jam'iyyar ta Ennahda ya musanta zargin cewa suna da hannu a kisan jagoran 'yan adawar.

Ya na mai cewa wadanda keda alhakin aikata kisan, na son su kawo cikas ne kawai ga demokradiyar Kasar.

Kamfanin jirgin saman Tunisia dai ya soke dukkanin tashi da saukar jiragensa a yau Juma'a, sakamakon wani yajin aiki da kungiyar kwadago mafi girma ta kasar ta kira.

Jama'a da dama na zargin jam'iyyar Islama ta Ennahada da wannan kisa.

Karin bayani