Birtaniya ta soki amfani da karfi a Masar

Image caption Rikici na kamari a Masar

Birtaniya ta yi kakkausar suka dangane da yin amfani da karfi da mahukuntan Masar suka yi wanda ya kai ga hasarar rayuka.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague ya yi kira ga mahukuntan kasar su kawo karshen tashe tashen hankulan wanda ya hada da amfani da makamai.

Ya bukaci hukunta wadanda ke da alhakin abin da ya faru, yana mai cewa wajibi ne a kare yancin gudanar da zanga zangar lumana.

Wani Minista a gwamnatin Birtaniya Alistair Burt wanda ya Isa birnin Alkahira a ranar Laraba ya shaidawa BBC cewa halin da ake ciki abin damuwa ne kwarai.

Yace Birtaniya na tuntubar bangarorin biyu kai tsaye. Shi ma kuma ya yi Allah wadai da tarzomar

" Yace muhimmin abu a yau shine dakatar da wannan tarzoma. Mun yi kakkausar suka da tarzomar da ta faru. Mun kuma la'anci amfani da harsasai akan masu zanga zanga wadanda ba sa dauke da makamai. Idan wannan abu bai kawo karshe ba lamarin zai cigaba da yin muni ne."in ji Alistair Burt.

Karin bayani