Masar:Limamin Al-Azhar da ElBaradei sun koka

Image caption Rikici a Masar

Manyan kusoshi biyu a kasar Masar wadanda suka goyi bayan kifar da Shugaba Muhammed Morsi sun yi Allawadai da kashe magoya bayansa da dama a artabu da sojoji.

Babban limamin masallancin Al-Azhar ya yi kira a gudanar da bincike, a yayinda mataimakin shugaban gwamnatin rikon kwarya, Muhammed ElBaradei ya ce anyi amfani da karfin daya wuce kima.

Ita dai gwamnati ta ce mutane 65 aka kashe lokacin da sojoji suka yi kokarin tarwatsa 'yan kungiyar Muslim Brotherhood wadanda suka kafa sansani a kusa da masallacin Rabaa al-Adawiya a birnin Alkahira.

Kungiyar Muslim Brotherhood kuwa cewa ta yi sojoji sun kashe mata akalla mutane 120.

Karin bayani