An kammala yakin neman zabe a Mali

Image caption An kammala yakin neman zabe a Mali

Wasu Sa'o'i kadan kafin zaben shugaban kasa a Mali, da dukkan alamu za a fafata tsakanin 'yan takara ashirin da bakwai da za su nemi a kada masu kuri'a.

Yankin Mopti ma, kamar shauran yankunan kasar, ya dau harami.

Hukumomin yankin dai sun ce komai ya kammala ta fuskar tsaro da tanadin kayayakin zabe.

Mopti dai na iyaka ne da Timbuktu, birnin da a baya masu tsattsauran ra'ayin musulunci suka mamaye.

Izuwa yanzu dai an zo karshen yakin neman zaben shugaban kasar da aka soma makwanni uku da suka gabata.

Bayan zagayen da suka yi a daukacin kasar, galibin 'yan takarar sun gudanar da tarurrukan gangaminsu na karshe a Bamako babban birnin kasar.

Karin bayani