An kashe sama da mutane 100 a Masar

Image caption An kashe mutane sama da dari a Masar

Rahotanni na cewa an kashe mutane sama da dari a rikicin da ya barke a birnin Alkahiran kasar Masar tsakanin magoya bayan hambararren Shugaban Kasar Mohammed Morsi da kuma dakarun tsaro.

An ambato wani likita na cewa an kashe mutane sama da dari kuma dubbai sun samu raunuka.

A wani rahotan da ba'a tabbatar ba; jam'iyyar 'yan uwa musulmi na cewa an kashe akalla mutanensu saba'in.

Wani wakilin BBC a wajen ya ce masu goyan bayan Mohammed Morsi wadanda suka taru a wurin wani masallaci mako da makonni na giggina shingaye, bayan sun yi fargabar cewa gwamnati na kokarin killace yankin.

Wannan tashin hankali dai ya biyo bayan gangamin da dukanin bangarorin biyu suka gudanar, bayan kiran da sojoji su ka yiwa mutanen kasar dasu fito domin yin zanga-zangar goya masu baya.

An rawaito Ministan cikin gida na Masar, Mohammed Ibrahim na cewa za a kawo karshen zaman durshen din da 'yan uwa musulmi suke yi a birnin ta fuskar shari'a.

Bayan wannan kalamai ne dai sojoji suka danna wajan masu zanga-zangar.

Karin bayani