Bam ya tashi a ofishin jakadancin Turkiya

Image caption Masu aikin kwana-kwana a Somalia

Wani dan kunar wake ya tada nakiyoyi a wajen wani gini dake dauke da ofishin jakadancin Turkiya a Mogadishu babban birnin Somalia.

Akalla mutane biyu sun rasu wanda ya hada da dan kunar bakin waken.

Kungiyar al-Shabaab ta ayyana cewa ita ta kai harin.

A baya dai ta sha kai hari akan cibiyoyin Turkiya wadanda ta zarga da yada akidar raba addini da harkokin gwamnati.

Turkiya dai na nuna goyon baya da kuma tallafawa gwamnatin Somaliya.

Karin bayani