'Yan Boko Haram sun kashe mutane 20 a Borno

Image caption Abubakar Shekau

Rundunar da ke aikin tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa a jihar Borno dake Najeriya, ta ce ana zargin 'yan kungiyar Boko Haram, sun kashe fararen hula ashirin a kauyen Dawashe da ke karamar hukumar Kukawa lokacin da 'yan sintiri suka kai musu hari.

Kakakin rundunar, Laftanar Haruna Muhammed Sani ya ce mutane da dama kuma suka samu raunuka, a harin wanda aka kai ranar asabar.

Wannan shi ne karon farko da 'yan kungiyar suka kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tun da aka fara azumin watan Ramalana.

Kakakin ya ce galibin wadanda abin ya rutsa da su masunta ne wadanda ke zuwa kamun kifi a kauyen kuma wadanda suka samu raunuka na ci gaba da karbar magani a wani wurin jiyyar marasa lafiya na soji dake garin Baga.

Sai dai yace an tura wata tawagar soji masu kai daukin gaggawa zuwa kauyen domin tabbatarda tsaron rayukkan da dukiyoyi mutane.

Karin bayani