An yi Allah wadai da kisan Masar

  • 28 Yuli 2013
Kasashen duniya sun fara Allah wadai da kisan Masar

Magoya bayan hambararren Shugaban Masar Mohamed Morsi na cigaba da yin zaman dirshan a wani masallaci dake gabashin birnin Alkahira, kwana guda bayan wani mummunan tashin hankali da aka gani tun lokacin da aka hambarar da tsohon shugaban kasar a farkon watan Yuli.

An kashe akalla mutane sittin da biyar a artabun da aka yi da jami'an tsaro, wanda ya faro bayan da aka kora cincirindon mutanen daga masallacin Rabaa- al Adawiya.

Ministan cikin gida na Masar, Mohammed Ibrahim ya musanta cewa 'yan sandan sun bude wuta akan masu boren, yana mai cewa hayaki mai sa hawaye kawai aka yi amfani da shi.

Mr Ibrahim ya kuma ce zaman dirshan din da suke yi wani hatsari ne ga jama'a, kuma a cewarsa za su yi maganin hakan ba tare da wani bata lokaci ba.

Yake cewa game da ainihin lokacin da za'a a tarwatsa zaman dirshan din da ake yi, akwai cikakken hadin kai tsakanin su da sojoji, kuma za su gudanar da taruka domin sa lokacin daya dace a soma tarwatsa su.

Karin bayani